<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>218</hymn_number>
<title>A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala LW218</title>
<lyrics>[V1]
 1) A cikin dukan halin da mu ke, da murna da wahala,
 Yabo na Allahna zan yi, zai riƙe zuciyata.

[V2]
 2) Bari mu girmama ka, Allah, mu ɗaukaka sunanka.
 Cikin wahala na yi kira, ka ba ni cetonka.

[V3]
 3) Rundunan Allah suna nan kewaye da adilai.
 Wanda ya ba da gaskiya, zai cece shi sarai.

[V4]
 4) Bari mu gwada ƙaunarsa, gwadawa za ta nuna
 Su ne masu albarka duka, masu gaskata ka.

[V5]
 5) Ku ji tsoronsa, tsarkaka, ba sauran tsoro kuma.
 Ku mai da aikinsa fa naku, muradinku zai biya.

[V6]
 6) Ga Allah Uba, Allah Ɗa, Ruhu Mai Tsarki kuma,
 Mu ba ka dukan ɗaukaka, ya Allah Triniti.</lyrics>
</song>